Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Saeed Khatibzadeh ya bayyana cewa, abin da Iran ta fi mayar da hankali a kan tattaunawar Vienna shi ne dage takunkumin da aka kakaba mata, kuma tawagar da ke tattaunawa ba za ta amince da wani abu da ya wuce abin da aka amince da shi a karkashin yarjejeniyar nukiliya da aka cimma ba a 2015.
Khatibzadeh ya jaddada cewa, batun tattaunawa a mataki mataki ko kuma shigar da wasu sabbin bukatu abu ne da ba za’a lamunta da shi ba.
Ya kara da cewa idan sauren bangarorin tattaunawar a Vienna, sun nuna da gaske su ke, to kuwa tabbas tattaunawar za ta yi armashi.
A jiya ne aka koma bakin tattaunawar ta Vienna da nufin farfado da yarjejeniyar nukiliyar Iran bayan shafe watanni na dakatarwa sakamakon zuwan sabuwar gwamnatin Iran.
342/